Gwamnan Legas

Gwamnan Legas shine shugaban Gwamnatin Legas. Gwamnan yana jagorantar bangaren zartarwa na Gwamnatin Jihar Legas . Wannan matsayi ya sanya mai riƙe shi a jagorancin jihar tare da ikon sarrafawa akan al'amuran jihar. Ana yawan bayyana Gwamna a matsayin ɗan ƙasa na ɗaya na jihar. Mataki na II na Kundin Tsarin Mulki na Najeriya ya ba da ikon zartarwa na jihar ga gwamna kuma ya bashi damar aiwatar da doka a jihar, tare da alhakin nada shugabannin zartarwa, na diflomasiyya, na doka, da na jami'an shari'a bisa amincewar mambobin Majalisar.


Developed by StudentB